Gwamnan Ebonyi ya ƙara albashin likitoci zuwa Naira 500,000

0
144

Gwamna Francis Nwifuru na jahar Ebonyi ya bayyana karin albashi da alawus na wata-wata ga sabbin likitocin da aka dauka aiki a jihar daga Naira 150,000 zuwa Naira 500,000.

Nwifuru ya sanar da hakan ne a ranar Litinin a Abakaliki, yayin kaddamar da shirin farfado da harkokin lafiya a jahar.

Haka kuma, ya kaddamar da kayan aikin asibiti masu darajar gaske don inganta kula da lafiyar al’umma.

Gwamnan ya jaddada cewa likitoci sun cancanci samun karin albashi domin su samu damar yin aiki yadda ya kamata tare da tallafawa iyalansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here