An ceto ƴan Najeriya da akayi safarar su zuwa Ghana da Mali

0
208

Hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ketare ta karɓi wasu ƴan kasar nan su 13 da akayi safarar su zuwa kasashen Ghana da Mali.

Mutanen sun haɗar da mata 12 da wani yaro ɗan shekaru 5.

A cewar wata sanarwa daga shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar tace shugabar hukumar, Abike Dabiri-Erewa, ce ta karɓe su.

‘Yan matan sun bayyana cewa an yaudare su da alƙawarin cewa za’a samar musu da aikin yi, amma daga baya suka fuskanci kansu ana tilasta musu yin karuwanci a kasashen na Mali da Ghana.

 Mun shiga ƙunci da cin zarafi da azabtuwa a hannun waɗanda suka yi safarar mu, inji yan matan.

NiDCOM ta miƙa waɗanda aka ceto ɗin ga hukumar NAPTIP domin tantance su da ba su kulawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here