Ƴan sanda sun harbe mai rubuta jarrabawar WAEC a Ibadan

0
157

Wani harbin kan mai uwa da wabi, yayi sanadiyar mutuwar wani dalibi mai rubuta jarrabawar WAEC ɗin da ake yi a halin yanzu. Lamarin ya faru a birnin Ibadan na jihar Oyo, a yau Talata.

Lamarin ya faru a hanyar zuwa kasuwar Gbagi dake ƙaramar hukumar Egbeda, lokacin da yan sanda suka bude wuta a kokarin su na kama wani mai lefi dake gudu a mota, inda harsashi ya kauce zuwa kan dalibin.

Rahotonni sun bayyana cewa dalibin da aka harbe ya kasance akan babur tare da mahaifinsa da kuma kannen sa, yayin da suke kan hanyar zuwa wajen rubuta jarrabawar.

Zuwa lokacin rubuta wannan labari ba’a ji ƙarin bayani daga jami’an yan sandan jihar ba, yayin da aka ajiye gawar mamacin a asibitin Adeoyo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here