Majalisa ta umarci a bada tsaro ɗan jaridar da ya bankado badakalar digiri ɗan kwatano
Majalisar Wakilai ta amince da bada kariya ta tsaro tsawon shekaru 10 ga wakilin Daily Nigerian, mai binciken ƙwaƙwaf, Umar Audu, biyo bayan fallasa yadda ake baƙalar kwalin kammala digiri a Kwatano, jamhuriyar Benin.
Binciken da Audu ya yi a boye ya bankado wani gungun mutane da ke taimaka wa ‘yan Najeriya siyan kwallon digiri da ba su yi karatun ba, wadanda da yawa aka sahale musu aiki a ma’aikatun gwamnati, ciki har da ma’aikatar ilimi suka wanke su ta hanyar damfara.
A halin yanzu dai kwamitin majalisar tarayya mai kula da jami’o’i, da fasaha, da harkokin cikin gida, da harkokin kasashen waje, da kuma ci gaban matasa, na binciken badakalar.
A zaman sa a yau Litinin, shugaban kwamitin, Abubakar Fulata, ya sanar da umarnin majalisar tare da yin kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da suka hada da hukumar tsaron fararen hula, NSCDC, da su tabbatar da tsaron Audu na tsawon shekaru goma masu zuwa.
“Muna godiya ga Audu bisa jajircewarsa, muna rokon ministan harkokin cikin gida da ya tabbatar da cewa jami’an tsaron NSCDC sun bayar da kariya da ake bukata tare da ‘yan sanda,” inji Fulata.
A cikin shaidar da ya bayar a gaban kwamitin, Audu ya bayyana yadda ya samu digirin digirgir na jami’ar Jamhuriyar Benin ba tare da ya je ya shiga a ji an koya masa ba kuma ma’aikatar ilimi ta amince da shi a kan kudi N40,000.