Jami’an tsaro sun Kama mai garkuwa da mutane zai tafi aikin hajji daga Sokoto

0
66

Jami’an rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) sun sake kama wani fitaccen ɗan ta’adda mai suna Sani Aliyu Galadi, a yayin da ya ke shirin tafiya aikin hajji daga jihar Sokoto.

Rahotonni sun ce wanda aka kama ɗin na cikin jerin waɗanda hukumomi ke nema ido rufe bisa zargin hannun sa a ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane

Zuwa yanzu dai jami’an tsaro na cigaba da gudanar da bincike akan sa.

Idan za’a iya tunawa ko a jiya Lahadi, Daily News 24 Hausa, ta kawo muku labarin yadda jami’an tsaro suka kama wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne zai tafi aikin hajji daga Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here