Boko Haram na ƙoƙarin ƙwace ƙaramar hukumar Marte—Zulum

0
94

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya roƙi gwamnatin tarayya ta samar da dabarun tsaron da zasu takawa mayaƙan Boko Haram da ISWAP birki daga yunkurin su na neman ƙwace ƙaramar hukumar Marte.

Zulum, ya nemi hakan a yammacin ranar Lahadi data gabata yayin da yakai wata ziyara zuwa yankin.

Kafin wannan lokaci mafi yawancin mutanen dake rayuwa a garin Marte sun gudu don neman tsira daga wani harin da yan ta’addan Boko Haram, suka kai a Juma’ar data gabata, sannan suka koma yankin Dikwa.

Gwamna Zulum, ya shaidawa manema labarai cewa ziyarar tasa wani yunkurin samar da ƙwarin gwuiwa ne ga al’ummar yankin, akan cigaba da bawa jami’an tsaro haɗin kai da manufar yaƙar rashin zaman lafiya.

Zulum ya ce a yanzu haka ƙaramar hukumar Marte na cikin hatsarin faɗa wa hannaun mayaƙan Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here