An kammala jigilar maniyyatan jihohi 12 zuwa Saudiyya

0
20

Hukumar dake kula da harkokin aikin hajji ta ƙasa ta bayyana cewa daga lokacin da aka fara jigilar maniyyatan hajjin bana zuwa yanzu an kammala kwashe maniyyatan jihohi 12, daga Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki da yawansu yakai 25,702.

Jihohin sun haɗar da Osun, Oyo,  Adamawa, Filato, Ekiti Imo, Legas, Abia da Edo.

Hukumar aikin hajjin tace anyi jigilar wadannan mutane cikin sahun jirgi 63 a kwanaki 10.

Kawo yanzu dai hukumar ta ce babu wata matsala da aka fuskanta tun bayan soma jigilar maniyyatan, inda a wannan shekarar hukumomi suka ce ƴan Najeriya 43,000 ne za su sauke farali.

An fara jigilar ne a ranar 9 ga wannan watan Mayun 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here