Ya kamata sarakuna da gwamnonin arewa su goyi bayan samar da ƴan sandan jihohi—Kawu Sumaila
Wakilin Kano ta Kudu a majalisar dattawa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya nemi masu riƙe da sarautar gargajiya da gwamnonin arewa su goyi bayan samar da ƴan sandan jihohi tare da ɗaukar batun da muhimmanci.
Cikin wata wasikar da Sanatan ya aikewa kungiyar gwamnonin arewa da sarakunan yankin, Kawu Sumaila, yace wannan kira da yayi abu ne mai ma’ana don kawar da batun addini, ƙabilanci, siyasa ko banbance banbancen dake tsakanin al’umma tare da tunkarar matsalar yankin.
Tuni dai wannan wasika taje hannun shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, wato Inuwa Yahaya, da kuma sarkin musulmi, don isar da wannan saƙo zuwa ga ɗaukacin gwamnonin arewa da sarakunan yankin.
Sanatan yace samar da ƴan sandan jihohi zai taimakawa arewa musamman a matsalolin tsaron da yankin ke ciki.