NDLEA ta kama tsofaffi masu fataucin miyagun ƙwayoyi

0
123

NDLEA ta kama tsofaffi masu fataucin miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta ce jami’anta sun kama wani dattijo mai suna Ayuba Ashiru, ɗan kimanin shekaru 80 da kilo 2.3 na miyagun ƙwayoyi.

Kakakin hukumar Femi Babafemi, ne ya sanar da hakan kamar yadda tashar talabijin ta Channels ta rawaito.

Sanarwar tace an kama wanda ake zargin a ranar 14 ga Mayun 2025 a yankin Dogarawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Garin jihar Kaduna bayan samun bayanan sirri a game da harkokin sa.

Sanarwar ta ce an taɓa kama tsohon akan laifin fataucin miyagun ƙwayoyi, sannan aka ɗaure shi shekara goma a  tsakanin shekarun 2014 zuwa 2024.

Ashiru, yace akalla yakai shekaru 46, a cikin wannan sana’a mummuna.

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa jami’an hukumar sun kama wata dattijuwa mai suna Uloma Uchechi Sunday mai shekara 82 da ƴarta mai shekara 32 mai suna Chisom Uchechi a jihar Abia da miyagun ƙwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here