Masu garkuwa sun kashe shugaban jam’iyyar APC

0
65

Masu garkuwa sun kashe shugaban jam’iyyar APC

Masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Ose a jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, bayan sace shi.

Shugaban ƙaramar hukumar Ose, Clement Kolapo Ojo, ne ya tabbatar da kisan cikin wata sanarwar da ya fitar da sanyin safiyar Lahadi.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Ose,  Oluwaseun Ogunniyi, ya fitar tace yan bindigar da suka sace shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar sun aikata wannan ɗanyen aiki bayan sakin wasu mutane biyu da suka kai kuɗin fansar sa, bayan sun riƙe su yayin kai kuɗi don sakin mutumin.

Zuwa lokacin rubuta wannan labari ba’a samu damar jin ta bakin Kwamishinan yan sandan jihar Ondo ba, Wilfred Afolabi, don jin ta bakin sa akan faruwar lamarin. Sai dai wani babban jami’in tsaro ya sanar da manema labarai cewa an tura wata tawagar jami’ai don nemo gawar Adepoyigi a dajin da aka kashe shi.

Idan za’a iya tunawa dai kafin kisan nasa masu garkuwar sun nemi a basu Naira miliyan 100, kafin sakin Adepoyigi, kafin daga bisani a daidai akan Naira miliyan 5.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here