Hatsarin kwale-kwale yayi sanadiyar mutuwar mutane 27 a yankin Gbajibo dake ƙaramar hukumar Kaigama a jihar Kwara.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun gamu da hatsarin yayin da jirgin ruwan su ya kife a hanyar su ta dawowa daga cin kasuwa. Hatsarin ya faru kwanaki 3 da suka gabata, watanni 7 bayan faruwar makamancin lamarin da ya kashe mutane fiye da 100 a jihar ta Kwara.
Ɗaya daga cikin mutanen da suka tsira daga hatsarin ya ɗora alhakin faruwar lamarin akan daukar mutane fiye da kima da matukin jirgin yayi, tare da kaɗawar iska mai ƙarfi wadda ta taimaka wajen kifewar jirgin ruwan.
Shugaban ƙaramar hukumar Kaigama, Abdullahi Danladi, ya ziyarci iyalan waɗanda abin ya shafa tare da jajanta musu.