Harin Bom ya kashe mutane da dama a sansanin sojojin Somaliya
Wani harin ɗan ƙunar bakin wake yayi sanadiyar mutuwar mutane 10 a wani sansanin sojoji dake Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, wanda tuni kungiyar Al-Shabab ta ɗauki alhakin harin.
Mahukunta daga fannin lafiya sunce an samu ƙarin mutane 30 da harin ya jikkata, bayan waɗanda suka rasu.
Wani ganau ya bayyana cewa ya ga lokacin da wani mutum ya fita daga cikin babur mai ƙafa uku, sannan ya afka cikin jama’a tare da tayar da bom ɗin.
Mayaƙan Al Shabaab sun sha kai hare-hare kan wuraren da ake ɗaukar sabbin jami’an soji.