An kama mai garkuwa da mutane zai tafi aikin hajji
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kama wani mutum da aka jima ana nema bisa zargin garkuwa da mutane, inda a yanzu aka same shi a sansanin alhazai na birnin tarayya Abuja.
Wata majiya daga sansanin itace ta tabbatar da hakan ga jaridar Daily trust.
Majiyar tace an samu nasarar kama ɗan ta’addan a yau Lahadi, yayin tantance maniyyatan da za su tafi ƙasa mai tsarki domin yin aikin hajjin bana.
Ɗan garkuwar mai suna Yahaya Zango, ya kasance mazaunin Paikon-Kore, ne dake karamar hukumar Gwagwalada da a Abuja.
Kamar yadda aka samu bayanai jami’an tsaro sun dade suna nemansa bisa zargin hannu a wasu hare-hare da garkuwa da mutane.