A’lummar Borno zasu yi azumi saboda ƙaruwar rashin tsaro

0
29

A’lummar Borno zasu yi azumi saboda ƙaruwar rashin tsaro

Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum, ya umarci a’lummar jihar baki ɗaya su ɗauki azumi don neman ɗaukin Ubangiji, ya kawo mafita akan matsalolin tsaron da suke ciki.

Zulum, ya nemi hakan yayin da yake yin jawabi ga ɗaukacin a’lummar Borno ta kafafen yada labarai a yau Lahadi.

Gwamnan jihar ta Borno, yace neman ɗaukin Ubangiji yafi komai muhimmanci a wannan yanayi da a’lumma suka tsinci kansu a ciki na zafafa kai hare haren yan ta’adda a Borno.

Ya kuma ɗauki alƙawarin karfafa gwuiwar masu bayar da tsaro na yan sa kai, da inganta ayyukan samar da bayanan sirri, don yaƙar rashin tsaron dake addabar Borno a baya bayan nan.

A kwana kwanan nan na tattauna da abokan hulɗar mu na gwamnatin tarayya a matakan tsaro daban daban, Kuma ina sanar da ku cewa yanzu shine lokacin da muke yin aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya fiye da kowane lokaci don kawo karshen rikicin da muke ciki, inji Zulum.

Shugaban ƙasa Tinubu, ya bayar da tabbacin cewa dole ne a shawo kan matsalolin tsaron da suka sake bijiro mana, a cewar gwamnan.

Daga karshe ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar jami’an sojojin da aka kashe a Borno sanadiyyar harin yan Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here