Ƴan sanda sun harbe ɗaliba yar shekaru 23

0
97

Jami’an ƴan sandan jihar Benue, sun harbe wata ɗaliba yar shekaru 23 mai suna Emmanuella Ahenjir, a shatale-talen Wurukum dake Makurdi, lokacin da taki tsayar da motar ta a wajen da yan sanda ke binciken ababen hawa a safiyar juma’ar data gabata.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar jami’an tsaron dake binciken ababen hawan sun yi bakin kokari wajen tsayar da ɗalibar amma hakan bai yiwu ba, wanda hakan ya sanya yan sanda bude wuta akanta har sai da harsashi ya fasa jikin Emmanuella daga nan kuma ta mutu bayan kai ta wani asibiti.

Emmanuella, ta kasance yar aji biyu a jami’ar tarayya ta garin Wukari dake jihar Taraba. Zuwa yanzu dai kisan ɗalibar ya haifar da cece kuce a Makurdi, a daidai lokacin da wasu ke neman a hukunta jami’an tsaron da suka harbe ba.

Kawo lokacin rubuta wannan labari ba’a samun damar jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan Benue Catherine Anene, ba dangane da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here