
Za’a siyo sabbin makaman yaƙi da ƴan ta’addan Najeriya—Christopher Musa
Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da cewa jami’an ta na yin matukar baƙin kokarin su wajen ganin sun kakkaɓe ƴan ta’adda da magance matsalolin tsaron da Najeriya ke fuskanta a kwana kwanan nan.
Hafsan hafsoshin tsaron ƙasa Janar Christopher Musa, ne ya sanar da hakan bayan wata ganawar da manyan jami’an tsaro suka yi da shugaban ƙasa Tinubu a yammacin ranar juma’a.
Musa, ya ƙara da cewa shugaba Tinubu ya umarci a samar da wadatattun kayan aiki ga jami’an tsaro wanda hakan zai inganta yaƙi da ɓata gari.
Tuni an samar da kayan yaƙi a yankin arewa maso gabas, don yaƙar masu ikirarin jihadi, inji Musa
A cewar babban hafsan, shugaban ƙasa Tinubu ya bayar da umurnin haɗa kai da kasashe masu makwabtaka da Najeriya da manufar taka burki ga ƴan ta’addan dake shigowa daga wasu ƙasashen.
Babban hafsan tsaron ya alaƙanta ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya da ƙara ƙaimi da ƴan ta’dda da kuma masu ikirarin jihadi ke yi a faɗin yankin Sahel, inda ya ce abin da ya sa ƙasar ke cikin matsin lamba shi ne rashin kyawun yanayin iyakokinta.