Kar ku amincewa labaran da ake yaɗawa a kaina—Kwankwaso

0
48
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar NNPP a shekarar 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi watsi da rahotannin dake cewa yana daf da komawa wata jam’iyya, da kuma batun shiga haɗaka da wasu jam’iyyu.

Kwankwaso ya bayyana hakan a matsayin labarin da ba gaskiya ba.

Wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafin sa na X, ɗan takarar shugaban ƙasar , ya ce raɗe-raɗin ba su da tushe balle makama.

A wannan lokaci na ja baya da yin magana akan abubuwan da suka shafi siyasar Najeriya, kuma zan cigaba da yin hakan har zuwa wani lokaci, inji Kwankwaso.

Akan hakan ya buƙaci al’umma da su amince da sakonni da suka fito daga shafukansa da kuma majiyoyi da aka yarda da su kaɗai ba daga wasu wurare na daban ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here