Gwamnatin Borno ta saka lokacin rufe sansanin ƴan gudun hijira na Muna

0
110

Gwamnatin Borno ta saka lokacin rufe sansanin ƴan gudun hijira na Muna

Gwamnatin jihar Borno ta saka lokacin rufe sansanin ƴan gudun hijira na Muna wanda ya shafe shekaru 10 anayin amfani dashi.

Gwamnan Jahar Borno, Farfesa Babagana Zulum Umara ya ce, nan da mako ɗaya mai zuwa za a rufe sansanin ‘yan gudun hijirar da ke dauke da ‘yan gudun hijira sama da 11,000.

Sansanin na Muna na daya daga cikin manyan sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar wanda aka samar shekaru 10 da suka gabata.

Gwamna Zulum ya bayyana rufe sansanin ne a lokacin da ya kai ziyara a sansanin a makon da ya gabata, inda ya bayyana munanan dabi’un da ake aikatawa a matsayin babban dalilin rufe sansanin.

Ya kuma kara da cewa, dole ne ‘yan gudun hijirar su koma gidajensu domin neman na kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here