Wasu mutane da ba’a san ko su waye ba, sun sace Sarki Obalohun na Okoloke a karamar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi, mai suna Oba James Dada Ogunyanda a fadarsa.
Anyi garkuwa da masaraucin ne a ranar Alhamis, wanda hakan ya haifar da zulumi ga al’ummar yankin wanda suka saba ganin sace mutane babu kakkautawa.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, wasu gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki fadar sarkin da ke garin Okoloke ne da misalin karfe 2 na tsakar dare.
Zuwa yanzu dai ba’a ji Æ™arin haske game da wanda suka sace shi ba, ko kuma neman kuÉ—in fansa.