Sojoji sun kwato shanu 1000, daga wajen ƴan ta’addan jihar Taraba

0
129

Dakarun sojin atisayen WHIRL STROKE, haɗin gwuiwa da dakarun atisayen SAFE HAVEN, sun kashe ƴan ta’adda biyu tare da kwato shanu dubu daya da suka sace a jihar Taraba.

Mai riƙon muƙamin mataimakin daraktan yaɗa labaran rundunar sojin ƙasa Kaftin  Oni Olubodunde, ne ya bayyana da hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a yau Juma’a, yana mai cewa sun samu nasarar yin wannan aiki ta hanyar samun sahihan bayanan sirri.

Yace sojojin sun ɗauki mataki akan wani rahoton dake cewa ƴan ta’addan da suke tafe akan babura da yawansu yakai 30 sun shiga jihar Taraba daga jihar Filato.

Oni Olubodunde, yace ƴan ta’addan sun farwa matsugunin Fulani dake Jebjeb, a ƙaramar hukumar Karim Lamido na jihar Taraba.

Rundunar sojin ta kara da cewa za’a gudanar da cikakken bincike don sanin asalin mamallaka shanun da aka kwato don mayar musu da dukiyar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here