Sojoji sun fatattaki mayaƙan Boko Haram daga dajin Sambisa

0
83

Rundunar sojin Najeriya takai wani harin ramuwar gayya zuwa ga maɓoyar mayaƙan Boko Haram dake dajin Sambisa, na jihar Borno, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar ƴan ta’adda da dama tare da lalata sansanin su.

Sojoji sun kai harin ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi yayin da suka farmake su.

Sojojin sun kai hari kan sansanonin ’yan ta’addar da ke Garin Malam Ali da Garin Glucose da kuma da Ukuba, waɗanda ke cikin Dajin Sambisa.

Wannan matakin da aka ɗauka ya biyo bayan jerin hare-hare da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Talata kan sansanonin sojoji guda uku a Rann da Gajiram da kuma da Dikwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu.

Majiyoyin soji, waɗanda suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana cewa haɗin gwiwar da aka yi da mayaƙan Civilian CJTF ya ɗauki sama da sa’o’i shida, daga misalin karfe 6 na safe a ranar Laraba har zuwa tsakar rana a ranar Alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here