Shugaba Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaron ƙasa

0
104

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yayi wata ganawa da manyan hafsoshin tsaron ƙasa da babban Sufeton yan sandan ƙasa a fadar sa dake birnin tarayya Abuja.

Ganawar tazo gabanin tafiyar Tinubu ƙasar Italiya don halartar kaddamar da sabon Fafaroma Leo XIV, a ranar Lahadi.

Waɗanda suka halarci taron ganawar sun haɗar da hafsan hafsoshin tsaron ƙasa Christopher Musa, hafsan sojin ƙasa Olufemi Oluyede, shugaban sojin sama Hassan Abubakar, shugaban sojin ruwa Emmanuel Ogalla, da Kayode Egbetokun, babban Sufeton yan sandan ƙasa.

Duk da cewa ba’a sanar da dalilin ganawar ba, amma ana kyautata zaton hakan baya rasa nasaba da ƙaruwar ayyukan rashin tsaro a sassan Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here