Rikici ya kashe mutane 10 a Filato

0
158
Map-of-Plateau-State

Ana sa ran mutum 10 aka kashe tare da sace shanu a wani sabon rikici da ya ɓarke a ƙaramar hukumar Riyom a jihar Plateau.

Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata amfanin gona da sace shanu da kashe wasu dabbobin.

Cikin wata sanarwa da rundunar soji ta ‘Operation Safe Haven’ ta fitar ta ce rikicin ya fara a ranar Litinin 12 ga watan Mayun da muke ciki, a lokacin da aka zargi wasu fusatattun matasa da kashe wasu shanu da suka yi zargin sun shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan da ke ƙaramar hukumar ta Riyom.

A ranar 13 ga watan ne kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Danchindo domin ramuwar gayya, tare da kashe mutum huɗu kafin su tsare bayan zuwan jami’an tsaro.

Haka kuma a ranar 14 aka zargi wasu mahara da kashe dabbobi 26 tare da raunata wasu a garin Darwat.

Daga baya kuma aka zargi wasu makiyaya da kai hari ƙauyen Wereng Kam tare da kashe mutum shida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here