Ɗaliban makarantu masu zaman kansu zasu fara karɓar bashin kuɗin karatu—Gwamnatin tarayya

0
52

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa zata fara bayar da tallafin bashin kuɗin karatu ga daliban dake yin karatu a makarantu masu zaman kansu.

Daraktan shirin bayar da tallafin bashin karatun Akintunde Sawyerr, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa akwai yiwuwar nan da shekaru uku masu zuwa dalibai a makarantun masu zaman kansu zasu fara samun wannan tallafi.

Sawyerr, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, lokacin da yake jawabi a wajen taron wayar da kan shugabannin makarantun gaba da sakandire da masu ruwa da tsaki akan shirin bayar da tallafin a jihar Enugu.

Daraktan yace babbar manufar shirin bayar da tallafin shine a bawa kowanne ɗan Najeriya damar cin gajiyar yin ilimi ko bashi da wadatar kuɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here