Ƙaruwar hare hare yasa an fara rufe makarantun jihar Katsina

0
228

Wani mummunan harin yan bindiga yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da sace shanu a yankin Dabaro na ƙaramar hukumar Faskari dake jihar Katsina.

Harin da ya faru a sanyin safiyar Alhamis ya sanya fargaba a zukatan a’lummar Dabaro, wanda hakan ya sanya wasu yin ƙaura don tsira da rayuwar su.

Ƙaruwar ayyukan rashin tsaro a Katsina ya tilasta rufe wasu makarantu a yankin Guga dake ƙaramar hukumar Bakori.

Wani mai sharhi akan harkokin tsaro mazaunin Katsina mai suna Bakatsine, ya tabbatar da labarin rufe makarantun, tare da nuna damuwa dangane da ƙaruwar rashin zaman lafiya a kudancin Katsina. 

Kawo lokacin rubuta wannan labari mahukuntan jihar Katsina basu ce komai ba dangane da harin ko kuma rufe makarantun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here