Majalisar wakilai tayi karatu na biyu akan ƙudirin dake neman a tilastawa kowanne ɗan Najeriya yin zaɓe in har yakai shekaru 18.
Tunda farko kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, ne ya ɗauki nauyin gabatar da ƙudirin.
Zuwa yanzu majalisar ta amince da karatu na biyu bayan da aka fuskanci wata muhawara mai zafi akan kudirin, yayin zaman majalisar na yau Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙudirin zai iya kunsar ɗaukar mataki akan duk ɗan ƙasar da yaƙi yin zaɓe da gangan.