Sabon rikici yayi sanadiyar mutuwar makiyayi da shanu fiye da 100 a Filato

0
65

Rahotonni sun bayyana cewa wasu hare haren da aka kaiwa ƙananun hukumomin Jos ta Kudu data arewa yayi sanadiyar mutuwar makiyayi ɗaya da shanu fiye da 100, a jihar Filato.

Mabanbantan ƴan ta’adda ne dai ke kai hare haren, wanda hakan ke tabbatar da yanayin taɓarɓarewar sha’anin tsaro, musamman a guraren da ake fama da matsalolin rashin zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma, wanda rikicin ke yin sanadiyar rayuwa da dukiyoyi.

Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar Filato Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi matasa ‘yan kabilar Berom daga ƙauyukan da abin ya shafa da hannu a hare-haren.

Sai dai shugabancin ƙungiyar matasan Berom ya musanta zargin, inda suka bayyana shi a matsayin ƙanzon kurege.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin farko ya faru da yammacin Talata a kauyen Gero da ke Jos na Kudu, yayin da na biyu ya faru da safiyar Laraba a kauyen Darwat da ke cikin ƙaramar hukumar Riyom.

A cewar Babayo, makiyaya uku sun jikkata a harin da aka kai a Gero inda ɗaya daga cikinsu yana karɓar magani a asibiti da ke Jos, yayin da sauran biyun ke jinya a asibitin Sojoji na Rukuba Barracks, Jos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here