Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji Janar Yakubu Gowon, mai ritaya yayi ikirarin cewa Najeriya ba zata sake komawa tsarin mulkin soji ba.
Gowon, ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja, yayin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da wani littafin daya ƙunshi tarihin rundunar sojin kasa da tasirin ta a tarihin Najeriya daga 1960 zuwa 2018.
Gowon ya ce duk da irin gudunmawar da sojoji suka bayar a tarihin Najeriya, musamman a lokacin yaƙin basasa da kuma samar da ababen more rayuwa bai kamata su sake tsoma baki a siyasa ba.
Yace dimokuraɗiyya tana tafe da wasu kura-kurai amma duk da haka itace hanyar samun cigaban ƙasa.
Yace dimokuraɗiyya ce ke bawa al’umma damar shiga harkokin mulki.