Majalisar wakilai ta tabbatar da cewa zata yi bincike akan tangarɗar da aka samu a jarrabawar JAMB, ta wannan shekara da hakan yayi sanadiyar samun sakamako mara daɗi.
Majalisar ta amince da kudurin yin binciken a zaman ta na ranar Alhamis, bayan da ɗan majalisa Adewale Adebayo daga jihar Osun, ya nemi hakan.
Idan za’a iya tunawa dai sakamakon jarrabawar JAMB ta wannan shekara ya bar baya da ƙura, wanda ɗalibai miliyan 1.5, suka gaza samun maki 200, sannan shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede, ya tabbatar da cewa sune suke da alhakin samun matsalolin da suka sanya aka samu rashin nasara daga ɗalibai.