Kabiru Alhassan Rurum ya fice daga NNPP
Ɗan Majalisa mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, a majalisar wakilai Kabiru Alhassan Rurum, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Shugaban Majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, ne ya karanta wasikar sauyin shekar Rurum a yayin a zaman majalisar.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da mai taimakawa ɗan majalisar a fannin kafafen yada labarai Fatihu Yusuf Bichi, ya fitar a yau Alhamis.
Rurum dai shine shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin sojojin sama.