Hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS tace yanayin hauhawar farashin kayayyakin masarufi ta ragu zuwa kaso 23.7 a cikin dari a watan Afrilu.
Hukumar tace a watan Maris hauhawar farashin ta tsaya akan kaso 24.23.
NBS ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis cikin rahotan da take fitarwa dangane da farashin kayayyakin da yan ƙasa ke siya don amfanin yau da kullum.