Gwamnatin Kano za ta tilastawa kamfanoni ɗaukar ma’aikata ƴan asalin jihar kaso 75 

0
100
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Kano, ta sanar da shirin samar da wata doka da zata tilasta ɗaukar yan asalin jihar aiki a kamfanoni masu zaman kansu dake jihar. Gwamnatin tace dokar ta ƙunshi cewa dole kaso 75 na ma’aikatan kamfanonin su kasance yan asalin Kano.

Akan hakan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya samar da wani kwamiti da manufar magance matsalolin da ƴan jihar ke fuskanta akan rashin ɗaukar su aiki daga kamfanoni, tare da dauko yan wasu jihohin.

 Shugaban kwamitin Dakta Ibrahim Garba, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan za’a miƙawa majalisar dokokin Kano daftarin dokar ɗaukar ma’aikatan, don magance matsalar ɗaukar ma’aikata a kamfanoni ba bisa ka’ida ba.

Yace manufar wannan yunkuri shine a magance matsalolin rashin aikin yi a tsakanin matasan jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here