Dalibai sun nemi a soke sakamakon jarrabawar JAMB baki ɗaya

0
82

Wasu daga cikin daliban da suka zana jarabawar neman gurbi a makarantun gaba da sakandire JAMB, sun nemi a soke sakamakon jarrabawar na wannan shekara baki ɗaya, biyo bayan amincewar da hukumar JAMB tayi na cewa an samu kuskure yayin jarrabawar, kuma itace da alhakin kuskuren.

Daliban sun shaidawa Daily trust, cewa an samu gagarumin rashin nasara a JAMB, biyo bayan matsalolin da aka fuskanta, kuma hukumar JAMB itace ke da alhakin haddasa wannan matsala.

Dalibai fiye da miliyan daya da rabi ne suka gaza samun maki da yakai 200, kuma hakan zai iya sanyawa mafi yawa daga ɗalibai su rasa damar shiga jami’a a wannan lokaci.

Wasu daliban sunce an samu matsaloli a cibiyoyin rubuta jarrabawar, sannan a wasu guraren ba’a bawa dalibai isasshen lokaci ba, wanda ake alaƙanta hakan da taimakawa ta fuskar faɗuwar daliban da aka samu.

A jiya Laraba, ne shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede, ya fashe da kuka yayin zantawar sa da manema labarai, inda ya tabbatar da cewa sune da alhakin rashin nasarar ɗalibai a jarrabawar, sannan ya nemi ayi musu afuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here