Ɗan majalisar tarayya daga Zamfara Aminu Jaji, yayi zargin cewa yan ta’addan jihar sun bawa karnukan su naman wasu jarirai biyu, bayan yin garkuwa da mahaifiyar su, inda ya bayyana hakan a matsayin babban abin tashin hankali sakamakon taɓarɓarewar sha’anin tsaro.
Jaji ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisar dokokin kasa, inda ya bayyana wani hoton yadda lamarin ya faru. Ya ce karamar hukumar Kaura Namoda ita kadai ta fuskanci hare-hare sama da 200 daga kungiyoyi masu dauke da makamai.
Jaji ya nuna ɓacin ran sa kan abinda ya kira da cewa gwamnatin tarayya ta kawar da kai ga abubuwan da suke faruwa duk da kiraye Kirayen neman ɗaukin da a’lummar jihar keyi. Bayan haka ɗan majalisar yace rashin zaman lafiya ya tilastawa mutane ficewa daga gidajen su don neman wajen tsira daga hare haren yan bindiga.
In har gwamnatin tarayya ta gaza ɗaukar matakin gaggawa lamarin zai wuce jihar Zamfara tare da kawo rashin tabbas a zaman lafiya a Najeriya baki ɗaya, inji Jaji
Jaji yace lamarin tsaro abu ne da ya shafi kowa don haka akwai bukatar kowa ya bada tasa gudummawar ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.