Shugaba Tinubu ya aikewa majalisa bukatar amincewa da kasafin Kuɗin Abuja 

0
112
Tinubu
Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya rubutawa majalisar dattawa wasikar neman amincewa da kasafin kuɗin birnin tarayya Abuja na shekarar 2025 da yawan yakai Naira triliyan 1.7

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan, yayin da ya karanto wasikar da shugaban kasar ya aikewa majalisa a yau Laraba.

A cewar wasikar kasafin kuɗin ya bayar da fifiko a fannin inganta harkokin lafiya, samar da aikin yi ga matasa, inganta noma da faɗaɗa walwalar jama’a.

Tinubu, yace abinda za’a mayar da hankali akai shine kasafin zai taimaka wajen fitar da a’lummar Abuja daga cikin ƙangin fatara, sai kammala ayyukan gina ƙasa da aka faro da kuma ƙirƙirar sabbin ayyuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here