Ko yanzu aka sake yin zaɓe Tinubu ne zai yi nasara—Oshiomhole

0
89
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, kuma dan majalisar dattawa daga jihar Edo, Adams Oshiomhole, ya bugu ƙirjin cewa ko a yau aka zo yin zaɓe, shugaban ƙasa Tinubu ne zai sake lashe kujerar shugabancin Najeriya.

Oshiomhole, ya bayyana hakan yayin da ake tattaunawa dashi a kafar telebijin ta Channels, game da ficewar Sanatocin jihar Kebbi su uku daga PDP zuwa APC.

Yace shugaba Tinubu, ya kai Najeriya wani babban matakin cigaba, yana mai cewa kafin zuwan Tinubu kan karagar mulkin Najeriya wasu manoman basu da ikon zuwa gonakin su saboda taɓarɓarewar sha’anin tsaro.

Oshiomhole, yace amma a yanzu an samu ingantuwar tsaron da manoma suna zuwa aikin su cikin kwanciyar hankali.

Ya kuma yi bayanin cewa sauyin shekar siyasa ba wani laifi bane, yana mai cewa madugun ƴan adawar Najeriya Atiku Abubakar, shine ya kamata ya fito ya rubuta littafi akan dalilan dake sanya yan siyasa sauya sheka, bisa hujjar sa ta cewa a baya Atiku, ya fice daga PDP zuwa ACN.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here