Gwamnatin tarayya ta ƙaryata batun sace kuɗin tallafin bashin karatu

0
83

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu gaskiya a zargin wawure Naira biliyan 71, daga cikin kuɗin tallafin bashin karatu da shugaban ƙasa Tinubu ya ƙirkiro.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan a yau Laraba, yana mai cewa babu wata almundahana da aka samu a shirin na NELFUND.

Alausa ya bayyana hakan yayin wani taro da yayi da shugabannin jami’o’in kasa, da asusun ba da lamuni na NELFUND.

Alausa ya kuma bayyana kalaman da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da cewa ba daidai ba ne.

Idan za’a iya tunawa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da dangogin su ta ƙasa ICPC, tace wani binciken data gudanar ya nuna cewa an wawure Naira biliyan 71.2 cikin biliyan 100, na tallafin bashin karatu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here