Dalibai 379,997 zasu sake rubuta jarrabawar JAMB

0
42

Dalibai 379,997 zasu sake rubuta jarrabawar JAMB

Hukumar shirya jarrabawar neman gurbi a makarantun gaba da sakandire JAMB ta tabbatar da cewa an samu kuskure yayin jarrabawar wannan shekara.

Shugaban hukumar JAMB Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya sanar da hakan lokacin da yake jawabi ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Yace dalibai 379,997, ne zasu da sake zana jarabawar a jihohi 5 dake yankin Kudu maso gabas da jihar Lagos, wanda nan gaba kaÉ—an za’a sanar da lokacin da zasu zauna sake rubuta sabuwar jarrabawar.

Oloyede, yace an samu waÉ—anda suka aikata cin dunduniyar JAMB yayin jarrabawar wannan shekara, yana mai cewa daga ranar Alhamis za’a fara aikawa É—aliban da abin ya shafa sakonni.

JAMB ta kuma nemi ayi mata afuwa bisa kuskuren da aka fuskanta a jarrabawar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here