An kama tarin masu laifi ɗauke da makamai a jihar Kogi

0
93

An kama tarin masu laifi da makamai a jihar Kogi

Rundunar ‘yansandan Jahar Kogi, ta kama mutane 239 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jahar. 

Kwamishinan ‘yansandan jahar, CP Miller Dantawaye, ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar da ke Lokoja a ranar Talata.

Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama, 66 ana zarginsu da aikata fashi da makami, 75 satar mutane, sannan 18 ana zargin da kisan kai.

Haka kuma, ya ce an kama mutane 21 da ake zargi da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, wasu 21 da an zarge su da aikata fyaɗe, guda shida an zarge su da aikin asiri, da kuma wasu 49 da ake zargi da aikata wasu manyan laifuka.

Makaman da aka samu sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyar, AK-49 guda biyu, harsasai sama da 400 da sauransu.

CP Dantawaye, ya ce rundunar ta fara horar da jami’anta domin ƙara musu ƙwarewa da ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here