Amurka ta cirewa Syria takunkuman data ƙaƙaba mata

0
84

Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasar sa ta janye ɗaukacin takunkuman data ƙaƙabawa ƙasar Syria.

Trump ya sanar hakan a lokacin da yake yin cikakken bayani akan matsayar Amurka dangane da cire takunkuman, yayin da yake jawabi a birnin Riyadh na Saudiyya lokacin da yakai ziyarar aiki.

Trump ya ce zai bai wa Syria damar tsayawa da ƙafafunta, bayan buƙatar gaggawa da Yarima Mohammed bin Salman ya miƙa masa.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da Trump ya soma yada zango a Saudiyya a rangadin kwanaki huɗu da yake yi a ƙasashen gabas ta tsakiya.

Trump ya ɗauki matakin da ya ba wa kowa mamaki na janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria, ana kwana guda kafin ganawarsa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar Ahmad Al-Sharaa a Saudiyya.

Takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba a lokacin da Assad ke kan karagar mulki, ya yanke ƙasar Syria daga tsarin hada-hadar kuɗi na duniya tare da daƙile zuba jari da cinikayyar ƙasashen waje, lamarin da ya kawo cikas ga yunƙurin sake gina ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here