‘Yan bindiga dun sace shugaban jam’iyyar APC, sun nemi Naira miliyan 100

0
150

Wasu ‘yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Ose,  Nelson Adepoyigi, a Jahar Ondo.

An sace shi ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Litinin, yayin da yake ƙoƙarin ajiye motarsa.

Wata majiya ta ce waɗanda suka sace shi sun shiga gidansa, tare dukansa da sanda kafin su tafi da shi.

Matarsa ta ji lokacin da yake ihu yake neman agaji, amma kafin ta fito, maharan sun tafi da shi.

Maharan sun tuntuɓi iyalinsa inda suka nemi a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa kafin sakin sa.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jahar Ondo, Olushola Ayanlade, ya tabbatar da sace mutumin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here