Mayaƙan ISWAP, sun sace sojoji daga sansanin su dake Borno
Wasu mayaƙan kungiyar ƴan ta’addan ISWAP sun kai wani ƙazamin hari a sansanin sojojin na Marte dake jihar Borno, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar sojoji da dama tare da kwashe makaman su. Bayan haka mayaƙan sun kuma sace wani adadin sojojin da ba’a tantance ba.
Kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito, majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa sannan suka cinna wa ma’ajiyar makamai da ke sansanin sojin wuta.
Mazauna yankin sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 3 na asuba, kafin wayewar garin ranar Asabar ne Boko Haram ta ƙaddamar da harin.
Wani soja da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, ISWAP ta ƙwace Marte, an kashe sojoji da dama, an kama wasu, amma wasu sun samu sun tsere zuwa Dikwa, inda runduna ta 24 take.
Yace an ta’addan sun ƙona tankokin yaƙi kuma sun kwashi makamai daga sansanin sojin.
Wani mazaunin Marte, gari mai nisan kilomita 38 daga Dikwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Dikwa, ya ce sun ji karar harbe-harben kuma daga bisani suka ga jirgin soji yana shawagi.
Ya ci gaba da cewa, abin takaici mayaƙan sun tsare mata da ƙananan yara da dama a Sabon Marte, amma wasu da dama sun samu tserewa zuwa Dikwa domin tseratar da rayuwarsu.