Kamfanin ƙera motoci na Nissan zai kori ma’aikata dubu 20

0
196

Kamfanin ƙera motoci na Nissan dake ƙasar Japan, a yau Talata ya bayyana cewa  yayi asarar kuɗin da yawan su yakai Dala biliyan 4.5, wanda hakan ya sanya shi ɗaukar matakin duba yiwuwar korar kaso 15 cikin ɗari na ma’aikatan sa dake faɗin duniya.

Kamfanin yayi gargadin cewa harajin da ƙasar Amurika take laftawa ƙasashe ka’iya bayar da gudummawa wajen ƙaruwar asarar.

Nissan, ya sanar da cewa a tsakanin shekarun 2024 zuwa 2025 yayi asarar yen biliyan 671, amma bai bayyana hasashen samun riba, a cikin shekarar 2025 ba, a daidai lokacin da kamfanin ke cewa yana sa ran yin kasuwancin yen triliyan 12.5, daga 2025 zuwa 2026.

Nissan, ya ƙara da cewa yanayin harajin da Amurka ke laftawa ƙasashe yasa ba zasu iya yin hasashen cikakken kasuwancin da zasu yi ba, da ribar da ake sa ran samu.

Haka ne ya sanya kamfanin yanke shawarar korar ma’aikata dubu 20, a cikin wannan shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here