Fashewar Bom ta kashe malamai biyu a jihar Borno

0
84
Borno
Borno

Fashewar wani Bom a hanyar Damboa zuwa Maiduguri, tayi sanadiyar mutuwar malaman Firamare biyu dake aiki ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, a Litinin data gabata.

Malaman masu suna Blessing Luka da Gideon Bitterleaf, sun gamu da ajalin su yayin da motar da suke tafiya zuwa Maiduguri ta taka Bom ɗin da aka ɗana a kan hanyar su. Ana kyautata zaton mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne suka ɗana Bom ɗin.

Shaidun gani da ido sunce waɗanda suka rasu a fashewar Bom ɗin sun kasance a cikin wata motar haya da ta dauko mangwaro.

Fashewar Bom ɗin ta kashe su nan take, inda wasu da ke cikin motar suka samu raunuka.

Jami’an tsaro sun killace wajen da lamarin ya faru, da kuma yin bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan abu don hukunta su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here