Shugaban NNPP na kasa yace Kwankwaso ne maci amana ba su Kawu Sumaila ba

0
75

Shugabancin jam’iyyar NNPP a matakin ƙasa ya ƙalubalanci Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, akan kalaman sa na cewa cin amana ne mutum ya ci zaɓe a karkashin wata jam’iyya sannan ya fice daga cikin ta zuwa wata jam’iyyar ta daban.

Kalaman na Kwankwaso ya zo bayan ficewar wasu mambobin majalisar dokokin kasa daga jihar Kano, inda suka fice daga NNPP zuwa APC.

Daga cikin yan majalisar akwai Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, dake wakiltar Kano ta Kudu, sai Kabiru Alhassan Rurum da Abdullahi Sani Rogo.

Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dr. Agbo Major, yace Kwankwaso bashi da hurumin yin magana a matsayin jam’iyyar NNPP, bisa hujjar cewa tun tuni jam’iyyar ta kori shi tare da magoya bayan kwankwasiyya.

Agbo Major, ya sanar da hakan a ranar Litinin lokacin da yake ganawa da manema labarai a jihar Lagos, tare da jaddada cewa waɗanda suka fice daga NNPP zuwa APC a jihar Kano, ba maciya amana bane, sai dai shi Kwankwaso ne mai cin amana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here