Rundunar ƴan sandan Kano ta ceto ɗan shekaru 75 da aka sace

0
40

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da kama wani mutum da take zargin mai garkuwa da mutane ne, tare da ceto wani tsoho ɗan kimanin shekaru 75 mai suna Abdulrahman Yunusa, a ƙaramar hukumar Bebeji.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa an kama mai garkuwar bayan samun bayanan sirri karkashin jagorancin wata tawagar da kwamishinan ƴan sanda CP Ibrahim Adamu Bakori, ya haɗa.

Yace bayan samun bayanan sirri, jami’an rundunar masu yaƙi da garkuwa da mutane suka kai mamaya zuwa maɓoyar yan garkuwar dake garin Bagau, inda aka samu nasarar kama wani ɗan shekaru 23 mai suna Musa Tukur, da ya fito daga ƙaramar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, inda aka same shi yana tsare tsohon da akayi garkuwa da shi

Yan sanda sun yi bayanin cewa an samu tsohon idon sa a rufe sannan an ɗaure hannuwan sa, bayan sato shi daga ƙaramar hukumar Soba ta Kaduna, tare da neman miliyan 20, a matsayin kuɗin fansar sa daga iyalan sa. Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta kara da cewa matashin da aka kama ya tabbatar da cewa yana da hannu a aikata sace tsohon.

Kawo wannan lokaci tuni an garzaya da Abdulrahman Yunusa, zuwa asibiti inda aka duba lafiyar sa, tare da miƙa shi hannu iyalan sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here