Matatar Dangote ta sake rage farashin man fetur

0
104

Matatar man fetur ta Dangote ta sake rage farashin litar man fetur daga Naira 835 zuwa Naira 825, a daidai lokacin da gasar kasuwanci ke cigaba da faɗaɗa a fannin mai na ƙasar nan.

Daga watan daya gabata zuwa yanzu matatar Dangote ta rage farashin man da Naira 45, kan kowacce lita, sakamakon cewa a baya ana siyar da litar man akan Naira 880.

Ragin farashin yazo a daidai lokacin da gwamnatin tarayya tace zata tabbatar da cinikayyar man fetur da takardar kuɗi ta Naira ga matatun cikin gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here