Matashi ya kashe saurayin ƙanwar sa a Kano

0
69

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani matashi da ya kashe saurayin ƙanwar sa, ta hanyar buga masa gora.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da hakan a shafin sa na Facebook.

Kiyawa yace matashin ya kashe saurayin ƙanwar tasa bayan da yaje zance, inda ya fito da gora tare da jibgawa mai shirin zama sirikin nasa.

 Zuwa yanzu an kama wanda yayi kisan don faɗaɗa bincike.

Karin bayani na tafe…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here