Lokacin mutuwar jam’iyyar PDP ya gabato—Ganduje

0
54
Ganduje

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya mayar da martani ga kalaman jigo a jam’iyyar PDP Sule Lamido, wanda yace nan gaba kaɗan rikici zai mamaye APC sannan manyan jiga-jigan ta ciki har da Gandujen zasu koma PDP.

Ganduje, yace babu gaskiya a zargin da Sule Lamido, yayi kuma batun nasa bashi da tushe balle makama.

Yayin da yake jaddada goyon bayan sa ga jam’iyyar APC, ya ce maimakon zuwa PDP nan ba da dadewa ba APC za ta karbi Sule Lamido don komawa cikin ta.

Ganduje, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Edwin Olofu ya fitar.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana wannan ikirarin a matsayin mara tushe kuma wanda hankali ba zai dauka ba, yana mai jaddada cewa babu dalilin da zai sa ya fice daga jam’iyya mai mulki zuwa jam’iyyar adawa.

Ganduje ya yi hasashen cewa PDP za ta ruguje a karshen 2025, saboda rigingimun cikin gida da jam’iyyar ke ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here