A tarihin Najeriya babu Shugaban da ya zubawa fanni noma kuɗi kamar Tinubu— Uba Sani

0
38

 

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya yi iƙirarin cewa a tarihin Najeriya ba’a taɓa samun Shugaban ƙasar da ya zuba jari a fannin noma, kamar yadda shugaba Tinubu yayi a cikin shekaru 2 kacal.

Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi yayin rabon tallafin rage raɗaɗi ga al’ummar jihar wanda shugaban ƙasa ya bayar.

Taron rabon tallafin ya gudana a ɗakin taro na Umaru Yar’adua, a ranar Lahadi, inda Uba Sani yace Tinubu yayi hakan da manufar rage talauci a arewa.Yace arewacin Najeriya musamman arewa maso yamma na fama da talauci da girmansa yakai kaso 65 zuwa 70 cikin dari. Sai dai a cewar sa shugaba Tinubu a cikin shekaru 2 ya samar da tsare tsaren tallafawa jama’a don rage talaucin.

Daga nan ya nemi gwamnatoci a kowanne mataki dasu goyi bayan manufofin gwamnatin tarayya akan kokarin kakkaɓe fatara da rashin aikin yi.

A nasa jawabin mataimakin shugaban ƙasa a fannin siyasa Alhaji Ibrahim Masari, wanda ya wakilci shugaban ƙasa Tinubu a wajen taron rabon tallafin ya jaddada cewa gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu, ta damu matuƙa wajen sanya walwala a zukatan al’umma, musamman yadda ya bayar da buhun shinkafa 12,000 da aka rabawa mutane a ɗaukacin ƙananun hukumomin jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here